37 Gama,
"A cikin ɗan lokaci kaɗan,
mai zuwan nan zai zo
ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38 Amma,
"Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.
In kuwa ya ja da baya,
ba zan ji daɗinsa ba."10.38 Hab 2.3,4
39 Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.