5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
"Ba zan taɓa bar ka ba;
ba zan taɓa yashe ka ba."13.5 M Sh 31.6
6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,
"Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.
Me mutum zai iya yi mini?"13.6 Zab 118.6,7