Pular para o conteúdo
Publicidade

Hebreus 8

6 Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.

7 Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. 8 Amma Allah ya sami mutane da laifi8.8 Za a fassara waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā laifi ya kuma ce wa mutane. ya ce,

"Ina gaya muku lokaci yana zuwa,

sa’ad da zan yi sabon alkawari

da gidan Isra’ila

da kuma gidan Yahuda.

9 Ba zai zama kamar irin alkawarin

da na yi da kakanni-kakanninsu

sa’ad da na kama hannunsu

don in fitar da su daga Masar ba,

domin ba su yi aminci da alkawarina ba,

sai na juya musu baya,

in ji Ubangiji.

10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila,

bayan lokacin nan,

in ji Ubangiji.

Zan sa dokokina a cikin zukatansu,

in kuma rubuta su a kan zukatansu.

Zan zama Allahnsu,

su kuwa za su zama mutanena.

11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba,

balle mutum ce wa ɗan’uwansa, Ka san Ubangiji,

domin dukansu za su san ni,

daga ƙaraminsu zuwa babba.

12 Gama zan gafarta muguntarsu

ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba."8.12 Irm 31.31-34

13 Ta wurin kira wannan alkawari "sabo," ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.

Veja também