16 Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa,9.16 Kalmar Girik guda da alkawari; haka ma a aya 17 dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, 17 domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. 18 Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini. 19 Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen. 20 Ya ce, "Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye."9.20 Fit 24.8
Publicidade