Yesu ya kira Filibus da Natanayel
43 Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, "Bi ni."
44 Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne. 45 Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, "Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf."