45 Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, "Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf."
46 Natanayel ya ce, "A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?"
Filibus ya ce, "Zo ka gani."
47 Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, "Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci."
48 Natanayel ya yi tambaya ya ce, "A ina ka san ni?"
Yesu ya amsa ya ce, "Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka."
49 Sai Natanayel ya ce, "Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila."
50 Yesu ya ce, "Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka." 51 Sai ya ƙara da cewa, "Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum."