Pular para o conteúdo
Publicidade

João 13

Yesu ya wanke ƙafafun almajiransa

1 Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.

2 Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman bashe Yesu. 3 Yesu kuwa ya san cewa, Uba ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma san cewa daga Allah ya zo, zai kuma koma wurin Allah; 4 saboda haka ya tashi daga cin abincin, ya tuɓe rigarsa ta waje, ya ɗaura tawul a ƙugunsa. 5 Bayan haka, sai ya zuba ruwa a cikin kwano, sa’an nan ya fara wanke ƙafafun almajiransa, yana sharewa da tawul wanda ya ɗaura.

6 Ya zo kan Siman Bitrus, wanda ya ce masa, "Ubangiji, kai za ka wanke ƙafafuna?"

7 Yesu ya amsa ya ce, "Yanzu ba ka fahimci abin da nake yi ba, amma nan gaba za ka gane."

8 Sai Bitrus ya ce, "Faufau, ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba."

Yesu ya amsa ya ce, "Sai na wanke ka, in ba haka ba, ba ka da rabo a gare ni."

9 Sai Siman Bitrus ya ce, "To, Ubangiji, ba ƙafafuna kaɗai ba har ma da hannuwana da kaina kuma!"

10 Yesu ya amsa ya ce, "Wanda ya riga ya yi wanka yana bukata wanke ƙafafunsa ne kawai; dukan jikinsa yana da tsabta. Ku kuwa kuna da tsabta, ko da yake ba kowannenku ba." 11 Gama ya san wanda zai bashe shi, shi ya sa ya ce, "Ba kowa ba ne yake da tsabta."

12 Da ya gama wanke ƙafafunsu, sai ya sa tufafinsa ya koma wurin zamansa. Ya tambaye su ya ce, "Kun fahimci abin da na yi muku? 13 Kuna ce da ni Malamda kuma Ubangiji,daidai ne kuwa, gama haka nake. 14 Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna. 15 Na ba ku misali domin ku yi yadda na yi muku. 16 Gaskiya nake gaya muku, ba bawan da ya fi maigidansa, ko ɗan saƙon da ya fi wanda ya aike shi. 17 Yanzu da kuka san waɗannan abubuwa, ku masu albarka ne, in kuka yi su.

Veja também