Pular para o conteúdo
Publicidade

João 14

21 Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi."

22 Sai Yahuda (ba Yahuda Iskariyot ba) ya ce, "Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu amma ba ga duniya ba?"

23 Yesu ya amsa ya ce, "Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.

Veja também