Yesu ya bayyana ga almajiransa
19 Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, "Salama tă kasance tare da ku!" 20 Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.
21 Sai Yesu ya sāke ce musu, "Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku." 22 Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, "Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan."