32 Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama. 33 Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai."
34 Sai suka ce, "Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi."
35 Sa’an nan Yesu ya furta cewa, "Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.