44 Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. 45 A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’6.45 Ish 54.13 Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina. 46 Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban. 47 Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.