48 Ni ne burodin rai. 49 Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu. 50 Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba. 51 Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai."