Pular para o conteúdo
Publicidade

João 6

53 Sai Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. 54 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe. 55 Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya. 56 Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa. 57 Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni. 58 Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada."

Veja também