Pular para o conteúdo
Publicidade

Yohanna 9

Yesu ya warkar da mutumin da aka haifa makaho

1 Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, "Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?"

3 Sai Yesu ya ce, "Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. 5 Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya."

6 Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. 7 Ya ce masa, "Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam" (kalman nan tana nufin "Aikakke"). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.

8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa yana bara, suka ce, "Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?" 9 Waɗansu suka ce shi mana.

Waɗansu kuwa suka ce, "A’a, ya dai yi kama da shi."

Amma shi ɗin ya ce, "Ƙwarai kuwa ni ne."

10 Sai suka ce, "To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?"

11 Ya amsa ya ce, "Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari."

12 Suka tambaye shi suka ce, "Ina mutumin yake?"

Ya ce, "Ban sani ba."

Veja também