6 "Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su. 7 Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. 9 Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."