Pular para o conteúdo
Publicidade

Josué 6

1 Ƙofofin Yeriko kuwa a kulle suke ciki da waje saboda Isra’ilawa, ba mai fita babu kuma mai shiga.

2 Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, "Duba, na ba ka nasara a kan Yeriko, duk da sarkinta da mayaƙanta. 3 Da kai da dukan sojoji, ku zaga birnin sau ɗaya kullum. Ku yi haka har kwana shida. 4 Ka sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni raguna su kasance a gaban akwatin alkawari. A rana ta bakwai sai ku zaga birnin sau bakwai, firistocin suna busa ƙahoni. 5 Sa’ad da kuka ji sun ɗauki dogon lokaci suna busa ƙaho, sai mutane gaba ɗaya su da murya su yi ihu da ƙarfi; katangar birnin kuwa za rushe, sai sojoji su haura, ko wanne nufi inda ya fuskanta kai tsaye."

6 Yoshuwa ɗan Nun kuwa ya kira firistoci ya ce musu, "Ku ɗauki akwatin alkawari, ku sa firistoci guda bakwai su riƙe ƙahoni su kasance a gabansa." 7 Sai ya umarci jama’a ya ce, "Mu je zuwa! Ku zaga birnin, masu tsaro da makamai su shiga gaban akwatin alkawarin Ubangiji."

Veja também