34 Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, "Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?"
35 Mala’ikan ya amsa ya ce, "Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi1.35 Ko kuwa Saboda haka, yaron da za a haifa za a kira shi mai tsarki Ɗan Allah. 36 ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida. 37 Gama ba abin da zai gagari Allah."
38 Maryamu ta amsa ta ce, "To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa." Sai mala’ikan ya tafi abinsa.