Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 12

15 Sai ya ce musu, "Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba."

16 Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, "Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai. 17 Ya yi tunani a ransa ya ce, Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?

18 "Sai ya ce, Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki. 19 Ni kuma zan ce wa raina, "Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa." 

20 "Amma Allah ya ce masa, Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?

21 "Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah."

Veja também