Pular para o conteúdo
Publicidade

Luka 17

14 Da ya gan su sai ya ce, "Ku je ku nuna kanku ga firistoci." Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.

15 Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16 Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.

17 Yesu ya yi tambaya ya ce, "Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18 Ba wanda ya dawo don yabi Allah, sai dai wannan baƙon?" 19 Sai ya ce masa, "Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai."

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também