Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 2

Haihuwar Yesu

1 A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. 2 (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) 3 Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.

4 Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. 5 Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.

Veja também