Pular para o conteúdo
Publicidade

Luka 2

22 Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji 23 (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, "Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji"2.23 Fit 13.2,12), 24 don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, "kurciyoyi biyu ko yan tattabarai biyu."2.24 Fir 12.8

25 To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi. 26 An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji. 27 Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci, 28 sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,

29 "Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari,

yanzu ka sallami bawanka lafiya.

30 Gama idanuna sun ga cetonka,

31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane,

32 haske don bayyanawa ga Al’ummai

da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila."

33 Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi. 34 Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, "An ƙaddara yaron nan zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, 35 ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki."

36 Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure, 37 ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu.2.37 Ko kuwa gwauruwa na shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a. 38 Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.

Veja também