40 Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, "Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? 41 Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba."
42 Sai ya ce, "Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka."
43 Yesu ya amsa, ya ce masa, "Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama."