Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 7

Bangaskiyar jarumin Roma

1 Bayan Yesu ya gama gaya wa mutanen dukan waɗannan abubuwa, sai ya shiga Kafarnahum. 2 A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. 3 Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa zo warkar da bawansa. 4 Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, "Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, 5 gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu." 6 Sai Yesu ya tafi tare da su.

Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, "Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba. 7 Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. 8 Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, Je ka,sai tafi, ga wani kuma in ce, Zo nan,sai zo. Nakan kuma ce wa bawana, Yi abu kaza,sai yi."

9 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, "Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba." 10 Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.

Veja também