Yesu ya tā da ɗan gwauruwa
11 Ba a daɗe ba, sai Yesu ya tafi wani garin da ake kira Nayin. Almajiransa da taro mai yawa suka tafi tare da shi. 12 Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. 13 Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, "Kada ki yi kuka."
14 Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, "Saurayi, na ce maka, tashi!" 15 Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
16 Sai tsoro ya kama su duka, suka yabi Allah, suna cewa, "Babban annabi ya bayyana a cikinmu. Allah ya zo domin yă taimaki mutanensa." 17 Wannan labarin game da Yesu, ya bazu ko’ina a Yahudiya da kewayenta.