Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 7

24 Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, "Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 25 In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da tufafi masu kyau ne? A’a, masu sa kayan tsada da suke cikin annashuwa, ai, a fada suke. 26 Amma me kuka je kallo? Annabi? I, ina kuma faɗa muku, ya ma fi annabi. 27 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa,

" Zan aiko da ɗan saƙona sha gabanka,

wanda zai shirya hanya, a gabanka. 7.27 Mal 3.1

28 Ina faɗa muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yohanna girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi."

29 (Dukan mutane, har da masu karɓar haraji, da suka ji kalmomin Yesu, sai suka yarda cewa hanyar Allah gaskiya ce, domin Yohanna ne ya yi musu baftisma. 30 Amma Farisiyawa da masanan dokoki, suka ƙi nufin Allah game da su, domin Yohanna bai yi musu baftisma ba.)

Veja também