31 Yesu ya ci gaba da cewa, "To, da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Kamar me suke? 32 Suna kama da yaran da suke zama a bakin kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,
" ‘Mun busa muku sarewa,
amma ba ku yi rawa ba,
Mun kuma yi muku waƙar makoki,
ba ku kuma yi kuka ba.’
33 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo, ba ya cin burodi, ba ya shan ruwan inabi, sai kuka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 34 Ɗan Mutum ya zo yana ci, yana sha, sai kuka ce, ‘Ga mai yawan ci, mashayi, da kuma abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ 35 Amma akan tabbatar da hikima ta gaskiya bisa ga dukan ’ya’yanta."
Mace mai zunubi ta shafe wa Yesu turare
36 To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur. 37 Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta,