27 Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. 28 Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, "Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!" 29 Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.
30 Yesu ya tambaye shi, "Mene ne sunanka?"
Sai ya amsa, "Tuli,"8.30 Lejiyon yana nufin Tuli. gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. 31 Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis.
32 A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. 33 Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
34 Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. 35 Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su.