Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 1

Mutum mai kuturta

40 Wani mutum mai kuturta1.40 Kalmar Girik da aka yi amfani da ita don kowace irin cutar da ta shafi fatar jiki ba lalle sai kuturta ba. ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, "In kana so, za ka iya tsabtacce ni."

41 Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, "Na yarda, ka tsabtacce!" 42 Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.

Veja também