Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 10

Bartimawus makaho ya sami gani

46 Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, "ɗan Timawus"), yana zaune a gefen hanya yana bara. 47 Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, "Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"

48 Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, "Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"

49 Yesu ya tsaya ya ce, "Ku kira shi."

Sai suka kira makahon suka ce, "Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka." 50 Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.

51 Yesu ya tambaye shi ya ce, "Me kake so in yi maka?"

Makahon ya ce, "Rabbi, ina so in sami ganin gari."

52 Yesu ya ce, "Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.

Veja também