Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 3

1 Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. 2 Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci. 3 Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, "Tashi ka tsaya a gaban kowa."

4 Sai Yesu ya tambaye su ya ce, "Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?" Amma suka yi shiru.

5 Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, "Miƙo hannunka." Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.

Veja também