3 "Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. 4 Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su. 5 Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi. 6 Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa. 7 Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba. 8 Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari."
9 Sai Yesu ya ce, "Duk mai kunnen ji, yă ji."