Pular para o conteúdo
Publicidade

Markus 6

21 A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. 22 Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa.

Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, "Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki."

Veja também