Yesu ya ciyar da dubu biyar
30 Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. 31 To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, "Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta."
32 Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa. 33 Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can. 34 Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.
35 A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, "Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. 36 Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci."
37 Sai ya amsa ya ce, "Ku, ku ba su wani abu su ci."
Suka ce masa, "Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum!6.37 Girik zai ci dinari ɗari biyu Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?"
38 Sai ya yi tambaya ya ce, "Burodi nawa kuke da su? Je ku duba."
Da suka duba, sai suka ce, "Biyar da kifi biyu."
39 Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40 Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. 41 Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. 42 Kowa ya ci, ya ƙoshi, 43 almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. 44 Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.