Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 7

11 Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,(wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12 sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13 Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa."

14 Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, "Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15 Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi."7.15 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da "marar tsabta." 16 Duk mai kunnuwan ji, yă ji

Veja também