Pular para o conteúdo
Publicidade

Markus 7

9 Ya kuma ce musu, "Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! 10 Gama Musa ya ce, Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,7.10 Fit 20.12; M Sh 5.16 kuma, Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.7.10 Fit 21.17; Fir 20.9 11 Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,(wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12 sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13 Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa."

Veja também