Pular para o conteúdo
Publicidade

Miquéias 5

An yi alkawarin mai mulki daga Betlehem

1 Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,5.1 Ko kuwa Ƙara ƙarfin katangarki, ya katangan birni

gama an kewaye mu da yaƙi.

Za su bugi kumatun mai mulkin

Isra’ila da sandar ƙarfe.

2 "Amma ke, Betlehem ta Efrata,

ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki5.2 Ko kuwa masu mulki a Yahuda,

daga cikinki wani zai zo domina

wanda zai yi mulkin Isra’ila,

wanda asalinsa5.2 Da Ibraniyanci fitowa daga

tun fil azal ne."5.2 Ko kuwa daga madawwamin kwanaki

3 Saboda haka za a yashe Isra’ila

har sai wadda take naƙuda ta haihu

sauran yan’uwansa kuma sun dawo

su haɗu da Isra’ilawa.

4 Zai tsaya yi kiwon garkensa

da ƙarfin Ubangiji,

cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.

Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa

za kai har ƙarshen duniya.

5 Zai kuma zama salamarsu.

Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari

suka tattake kagarunmu,

za mu da makiyaya bakwai,

har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.

6 Za su yi mulkin5.6 Ko kuwa ragargaza ƙasar Assuriya da takobi,

ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.5.6 Ko kuwa Nimrod a bakin ƙofofinta

Zai cece mu daga hannun Assuriyawa

sa’ad da suka kawo wa ƙasarmu hari

suka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.

7 Raguwar Yaƙub za kasance

a tsakiyar mutane masu yawa

kamar raɓa daga Ubangiji,

kamar yayyafi a kan ciyawa,

wanda ba ya jiran mutum

ko kuma dakata wa ɗan adam.

8 Raguwar Yaƙub za kasance tare da al’ummai,

a cikin mutane masu yawa,

kamar zaki a cikin sauran namun jeji,

kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,

wanda yake tattaka kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,

ba kuwa wanda zai cece su.

9 Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,

za a hallaka maƙiyanka duka.

10 "A wannan rana," in ji Ubangiji

"Zan hallaka dawakanku daga cikinku,

in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.

11 Zan hallaka biranen ƙasarku

in yi rugu-rugu da dukan katangunku.

12 Zan kawar da maitarku,

ba za a ƙara yin sihiri ba.

13 Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa

da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,

nan gaba ba za ku ƙara rusuna

wa aikin hannuwanku ba.

14 Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku5.14 Wato, alamar alliyar Ashera

in kuma rurrushe biranenku.

15 Zan yi ramuwa cikin fushi da hasala

a kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba."

Veja também