22 Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, 23 "Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel"1.23 Ish 7.14 (wanda yake nufin "Allah tare da mu").
24 Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. 25 Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.