Kaiton biranen da ba su tuba ba
20 Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. 21 "Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. 22 Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku. 23 Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau. 24 Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a."