Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 12

Alamar Yunana

38 Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, "Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka."

39 Sai ya amsa ya ce, "Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana. 40 Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.

Veja também