Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 24

3 Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, "Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?"

4 Yesu ya amsa, "Ku lura fa, kada wani ruɗe ku. 5 Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, Ni ne Kiristi,za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 6 Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.

Veja também