Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 5

3 "Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,

gama mulkin sama nasu ne.

4 Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

gama za a yi musu ta’aziyya.

5 Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u,

gama za su gāji duniya.

6 Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,

gama za a ƙosar da su.

7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,

gama za a nuna musu jinƙai.

8 Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,

gama za su ga Allah.

9 Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,

gama za a kira su ya’yan Allah.

10 Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,

gama mulkin sama nasu ne.

11 "Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. 12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

Veja também