Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 7

Magini mai hikima da marar hikima

24 "Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa."

Veja também