Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 8

Warkar da mutum biyu masu aljanu

28 Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa8.28 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Gergesenawa; waɗansu kuma Gerasenawa ne a nan (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. 29 Suka yi ihu suka ce, "Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?" Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yi?

30 Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. 31 Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, "In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan."

32 Ya ce musu, "Ku tafi!" Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. 33 Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. 34 Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi bar musu yanki.

Veja também