20 A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa. 21 Ta ce a ranta, "Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke."
22 Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, "Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke." Nan take macen ta warke.