4 Sai sarki ya ce mini, "Me kake so?"
Sai na yi addu’a ga Allah na sama, 5 na kuwa ba wa sarki amsa, na ce, "In ya gamshi sarki, in kuma bawanka ya sami tagomashi a idonka, bari ka aike ni in tafi ƙasar Yahuda, birnin da aka binne kakannina, domin in sāke gina shi."