Pular para o conteúdo
Publicidade

Números 10

33 Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don samo musu masauƙi. 34 A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.

35 Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce,

"Ka tashi, ya Ubangiji!

Ka sa maƙiyanka su warwatse;

masu ƙinka kuma su gudu a gabanka."

36 Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce,

"Ka komo, ya Ubangiji,

a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila."

Veja também