Pular para o conteúdo
Publicidade

Ƙidaya 36

Gādon ya’yan Zelofehad mata

1 Sai shugabannin gidajen iyalan Gileyad ɗan Makir, ɗan Manasse, waɗanda suka fito daga kabilar zuriyar Yusuf, suka zo, suka yi magana a gaban Musa da shugabanni, shugabannin iyalan Isra’ilawa. 2 Suka ce, "Sa’ad da Ubangiji ya umarce ranka daɗe, raba ƙasar gādo ga Isra’ilawa ta wurin ƙuri’a, ya umarce ka, ka ba wa ya’ya matan nan na Zelofehad ɗan’uwanmu gādonsa. 3 To, a ce sun auri mutane daga waɗansu kabilan Isra’ilawa fa; ka ga, za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura ke nan. Ta haka za a ɗebe sashe daga gādon da aka ba mu ke nan. 4 Sa’ad da Shekara ta Murnar Isra’ilawa ta kewayo, za a haɗa gādonsu da na kabilan mutanen da suka aura, a kuma ba su mallakar gādon da aka ɗebe daga kabilar kakanninmu."

5 Ta wurin umarnin Ubangiji, Musa ya ba Isra’ilawa wannan umarni, "Abin da kabilar zuriyar Yusuf suke faɗi, daidai ne. 6 Ga abin da Ubangiji ya umarta saboda ya’ya matan nan na Zelofehad. Za su iya auri duk wanda suka ga dama, muddin sun yi aure a cikin kabilar kakanninsu. 7 Ba gādon Isra’ilan da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowane mutumin Isra’ila zai riƙe gādonsa na kabilar da ya gāda daga kakanninsa. 8 Kowace ya wadda ta ci gādon ƙasa, a kowace kabilar Isra’ilawa, dole auri wani cikin kabilar kakanninta, saboda kowane mutumin Isra’ila mallaki gādon kakanninsa. 9 Ba gādon da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowace kabilar Isra’ilawa za riƙe mallaka da ta gāda."

10 Saboda haka ya’yan Zelofehad mata suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa. 11 Ya’yan Zelofehad mata, Mala, Tirza, Hogla, Milka da Nowa, suka auri ya’yan yan’uwa na gefen mahaifinsu. 12 Suka yi aure cikin kabilar zuriyar Manasse ɗan Yusuf, gādonsu kuwa ya kasance a cikin iyali da kuma kabilar mahaifinsu.

13 Waɗannan su ne umarnai da ƙa’idodin da Ubangiji ya ba wa Isra’ilawa ta wurin Musa, a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também