Publicidade

Provérbios 1

1 Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.

2 Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;

don ganewa kalmomi masu zurfi;

3 don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,

kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

4 don sa marar azanci yi hankali,

sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

5 bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,

bari masu tunani kuma su sami jagora,

6 don su fahimci karin magana da kuma misalai,

kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.

7 Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

amma wawaye1.7 Kalmomin Ibraniyancin da aka rubuta wawa a cikin Littafi Karin Magana, da kuma ko’ina a cikin Tsohon Alkawari sau da yawa, yana nufin wani wanda ya rasa cikakken ɗa’a ne. sun rena hikima da horo.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-