Jan kunne game da ƙin hikima
20 Hikima tana kira da ƙarfi a kan titi,
tana ɗaga muryarta a dandalin taron jama’a;
21 tana kira da ƙarfi a kan tituna masu surutu,1.21 Da Ibraniyanci; Seftuwajin / a bisa katanga
tana yin jawabinta a hanyoyin shiga gari.
22 "Har yaushe ku da kuke marasa azanci1.22 Kalmar Ibraniyancin da aka rubuta marar azanci a cikin Littafin Kari Magana gaba ɗaya tana nufin marar ɗa’a da kuma wanda yana aikata mugunta ne. za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci?
Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku
wawaye kuma ku ƙi ilimi?
23 Da a ce kun saurari tsawatata,
da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata
in kuma sanar da ku tunanina.