Pular para o conteúdo
Publicidade

Provérbios 4

Hikima ce mafi girma duka

1 Ku saurara ya’yana ga koyarwar mahaifinku;

ku mai da hankali, ku sami fahimi.

2 Ina ba ku sahihiyar koyarwa,

saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.

3 Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina,

yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,

4 ya koya mini ya ce,

"Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka;

ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.

5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;

kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.

6 Kada ka ƙyale hikima, za kuwa tsare ka;

ka ƙaunace ta, za kuwa lura da kai.

Veja também